Abuja – Jam’iyyar hamayya Peoples Democratic Party (PDP) tace ta kammala duk wasu shirye-shiryen domin fara yaƙin neman zaɓe na shekarar 2023, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan duba Ofishin kamfen Atiku Abubakar da ke Abuja, Darakta Janar na kwamitin kamfen shugaban ƙasa a PDP, Aminu Tambuwal, yace zasu fara kamfe a Uyo, babban birnin Akwa Ibom ranar Litinin.
Da izinin Allah, zamu fara yaƙin neman zaɓe ranar Litinin mai zuwa a Uyo, jihar Akwa Ibom. Am kammala dukkanin wasu shirye-shirye tsaf domin tabbatar da taro ya tashi lafiya.”
“Kamfem mu zai kasance kan batutuwa masu muhimmanci. Zamu tallata ‘yan takarar mu bisa abubuwan da suka fito a zahirance, waɗanda muke ganin sune hanyar maslaha.”