Yara 62 ne suka fita zakka a karamar hukumar ungoggo

A safiyar wannan rana ne ta lahadi daliban makarantar madinatul ahbab wal talamiz fi rihabul qur’an dake rafin malam din karamar hukumar ungoggo ne suka gudanar da bikin yayi daliban da suka samu ikon sauke littafin Allah SWA

Abba mustafa da aisha musa ne suka wakilci ragowar daliban wajan bayyana irin farin cikin da suka tsinci kansu a wannan rana

Wakilin magajin malam hakimin karamar hukumar Shehu abdulkadir Ahmad
Dagacin garin mustafa dahiru da shugaban makarantun ahbabu na kasa tijjani dan Almajiri dukkanin su sun nuna farin cikin su hadi da yabawa malaman daliban na irin wannan namijin aiki da sukai tare da kara kira ga iyaye dasu dinga sauke hakkin dake kansu musamman wajan sauke nauyin biyan kudin makaranta

A karshe shugaban makarantar malam habibu abubakar Yace an kafa wannan makaranta a shekara ta 2018 ta fara da dalibai 21 maza 13 mata 8 ya yabawa iyayen da suke bibiyar karatun “ya”yan su ta hanyar ganin yadda suke kokari

A karshe yayi kira ga duk wanda Allah yasa yana da rabon samun darajar da Allah yake baiwa masu hidimtawa ilimi dasu kawo wa wannan makaranta daukin samun matsuguni na dindindin duba da cewa a halin yanzu suna zaune a matsugunin aro

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments