Russia ta sake kai mummunan hari a kudancin Ukraine

Wani harin makami mai linzami da Rasha ta kai cikin dare ya kashe mutane 17 a Zaporizhzhia, a wani mummunan hari na baya bayan nan da aka kai yankin da ke kudancin Ukraine.

Anatoliy Kurtev, sakataren majalisar birnin Zaporizhzhia, ya wallafa a shafinsa na Telegram cewa, bayan harin makami mai linzami a Zaporizhzhia, akalla gidaje 20 da kuma gine-ginen benaye kusan 50 sun lalace. Mutane 17 ne suka mutu, ya zuwa yanzu.

Ya kara da cewa an lalata cibiyoyin ilimi hudu.

Zelensky da jami’in yankin Oleksandr Starukh sun bayar da adadin wadanda suka mutu ya kai 12, yayin da na baya-bayan nan ya ce akwai yiwuwar wasu karin wadanda abin ya rutsa da su na karkashin baraguzan ginin yayin da aka kaddamar da aikin neman ceto.

Akalla mutane 17 ciki har da wani yaro ne suka mutu a yayin da wasu makamai masu linzami na Rasha bakwai suka afkawa Zaporizhzhia kafin wayewar gari a ranar Alhamis, kamar yadda hukumomin Ukraine suka sanar a wani adadi da aka yi wa kwaskwarima ranar Asabar.

Zaporizhzhia dai na kusa da fagen daga inda dakarun Kyiv ke kai wani gagarumin farmaki kan sojojin Rasha.

Manyan wuraren da ke da kamfanonin da ke karkashin ikon Ukraine yana cikin yankin Zaporizhzhia, wanda kuma ke da tashar nukiliyar da Rasha ta mamaye, inda aka yi ta luguden wuta.

Moscow ta yi ikirarin mamaye yankin duk da cewa dakarunta ba su da iko da shi baki daya.

Ukraine ta ce akalla mutane 30 ne suka mutu a makon da ya gabata, lokacin da aka kai har ikan wani ayarin motocin farar hula a yankin Zaporizhzhia alhakin da aka dora wa Moscow.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments