Yan bindiga sun hallaka wani mai sarautar gargajiya na Orsu Obota, Eze Victor Ijioma a karamar hukumar Oguta da ke jihar Imo.
Marigayin basaraken an kashe shi ne a yankin Isama da ke gundumar Mgbele a karamar Hukumar sa
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa masu sarautar gargajiya biyu ne aka kashe a hare-hare daban-daban a ranar Alhamis 25 ga watan Mayu.
Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan sun tare marigayin ne a kwanar Umuamaka kusa da garin I zombie inda suka kashe shi a cikin motarsa kuma suka cinnawa gawarsa wuta.