Shugaban ƙasa Muhammad Buhari a shirye-shiryen sa na barin gado, zai gabatar da jawabin ƙarshe ga ƴan Najeriya ranar Lahadi, 28 ga watan Mayu da misalin ƙarfe 7 na safe.
Hadimin shugaba Buhari, Bashir Ahmad, shine ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter, ranar Asabar 27 ga watan Mayu
Jawabin zai zo ne ana sauran ƴan sa’o’i kaɗan shugaba Buhari ya miƙa ragama mulkin ƙasar nan a hannun Bola Tinubu