Mazauna ƙauyukan Kaduna sun nuna damuwarsu tare da ankarar da cewa ‘yan bindiga da ke tsere wa luguden wutar da ake musu a Zamfara na samun mafaka a dazukan da ke kusa da su.
Garuruwan da ke iyaka tsakanin Zamfara da Kaduna ne suka fitar da wannan korafi, tare da cewa suna ganin ‘yan bindiga na yi musu shawagi.
Mazauna kauyen Damari a karamar hukumar Birnin Gwari sun ce ‘yan bindiga na shigar garuruwansu da tsakar rana.
Jaridar Daily Trust ta rawaito wani mai suna Saeed dake zaune a kauyen na Damari na cewa tun ranar Talata ‘yan bindiga ke kwarara zuwa cikin dajin Kudu run dake makoftaka da garin nasu
Haka zalika shi ma wani mazaunin yankin ya shaida wa manema labarai cewa ‘yan bindigar na yi musu barazanar garkuwa da manoma.
Da fatan wannan kira ko kuma ankararwa zata yi amfani