Rahotanni daga mabanbantan jaridu na cewa, hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta kasa (FAAN), ta bayar da umarnin gaggauta kwashe dukkan jiragen saman dake babban filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake birnin Abuja,
Gabanin bikin kaddamar da sabuwar gwamnati da aka shirya gudanarwa a ranar 29 ga watan Mayun shekarar nan ta 2023. FAAN ta ce an dauki wannan mataki ne domin inganta harkar tsaro, a filin jirgin saman a yayin rantsar da shugaban kasa mai jiran gado.
Da yake tsokaci kan wannan umarni, tsohon manajan daraktan hukumar kula da sararin samaniya Kyaftin Roland Iyayi ya bayyana cewa, akasarin jiragen da aka ajiye a babban filin jiragen sama da ke Abuja, jiragen sama ne na daidaikon mutane, da na wasu masu arziki, da na wasu kamfanonin jiragen sama, kuma galibin jiragen ba su da karfin jigilar fasinjoji.
A cewar sa hakan na nufin aiwatar da umarnin kwashe su duka daga filin zai zama aiki mai wahala kwarai