Faransawa biyu gwamnatin Tehran ta sallama daga gidan yarin kasar bayan sun shafe lokaci suna zaman kurkuku kan zarge-zargen take wasu dokokin kasar.
Wasu Turawa biyu na kan hanyarsu ta komawa Faransa, bayan da aka sako su daga wani gidan yarin Iran a wannan Jumma’ar.
Bafaranshe Benjamin Briere mai shekaru 37 da haihuwa, ya kwashe shekaru uku a gidan yari kan laifin daukar hotuna a wasu wuraren da gwamnatin Tehran ta haramta
Bayan hakan ne aka yanke wa dan kasar Ireland mai jini da Faransa Bernard Phelan hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari bisa laifin leken asiri, dan shekaru 64 da haihuwar, ya yi zaman gidan yarin na watanni bakwai kafin a cimma matsaya a tsakanin Iran da Faransa.
Jim kadan da bayar da umarnin su bar kasar, Shugaba Emmanuel Macron na Faransan ya wallafa labarin a shafinsa na Twitter, ya na mai baiyana jin dadinsa tare da cewa, sabon babi kasashen biyu suka bude na fatan gina dangantakar aminta da juna