Daga Adamu Dabo
Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin sabbin mashawarta
1 Engineer Sulaiman Sani mashawarci na musamman kan harkokin noman Rani
2 Abdullahi Shuaibu mashawarci na musamman kan harkokin fansho
3 Yusuf Imam Shuaibu mashawarci na musamman kan harkokin matasa da wasanni
4 Sadiya Abdu Bichi mashawarciya ta musamman harkokin mata da yara da Kuma gajiyayyu
5 Dr Nura Jafar Shanono mashwarci na musamman kan harkokin Samar da ruwan sha
6 Sanusi Sirajo Kwankwaso mashawarci na musamman kan harkokin siyasa
Gwamna Yusuf ya Kuma amince da nadin shuwagabanin wasu ma’aikatan jihar kano
1. Engineer Faisal Mahmud Kumbotso MD KAROTA
2. Alhaji Abdullahi Rabiu MD Housing Corporation
3 Alhaji Ahmadu Haruna Danzago MD REMASAB
4 Hon Hisham Habib MD Radio Kano
Wakilinmu dake fadar Gwamnati jihar Kano Adamu Dabo adamu ya bamu labarin cewar sabbin nade naden na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mukaddashin Mai magana da yawun Gwamnan kano Hisham Habib da aka rabawa manema labarai
Sanarwar ta ce sabbin nade naden nasu ya fara aiki nan take