Mista Romanus Ejikeme, mahaifin Mmesoma Ejikeme, dalibar da ta jirkita sakamakon jarrabawarta na JAMB, ya fito fili ya nemi gafarar Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a (JAMB) da ma ‘yan Najeriya baki daya.
Kamar yadda aka gani a wata hira da gidan talabijin na Najeriya (NTA), ya ce da far dai ‘yarsa ta shirga masa karya don haka yanzu da ya san gaskiya, yana fatan JAMB ta yafewa ‘yarsa.
A baya, yarinyar ta yi ikirarin cewa, ta lashe sakamako mafi yawa na UTME na 2023, lamarin da ya jawo cece-kuce bayan da hukumar JAMB ta ce ba haka bane.
Daga bisani, an janye sakamakon da ta samu na maki 249, bayan ta yada cewa, ta samu maki 362.
JAMB ta bayyana cewa, tabbas tana da hujjar cewa yarinyar ta jirkita sakamakon ne, kana ba wannan ne karon farko da matasa ke yin haka ba.
Hakan ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda wasu ke ganin hukumar na da matsalar sauya sakamakon Ta amsa cewa ta jikita sakamakon
A yau ne aka samu labarin cewa, dalibar ta bayyana gaskiya, inda tace da kanta ta jirkita sakamakon jarrabawar.
Wannan na fitowa ne daga wani kwamitin da gwamnan jihar Anambra ya hada, inda suka titsiye yarinyar tare da jin gaskiyar abin da ke faruwa.