Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin shugabannin wasu hukumomi da ma’aikatun gwamnati.
Hakan na kunshe ne cikin wata Sanarwa da babban sakataren yada labaran gwaman, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa
Wadanda aka nada sun hadar da
1. Injiniya Ado Ibrahim Umar, Manajan Darakta na Kamfanin Wutar Lantarki na Kano (KHEDCO)
2. Alh. Auwalu Mukhtar Bichi, Manajan Daraktan Kamfanin Zuba Jari na kano.
3. Dr. Farouq Kurawa, Manajan Daraktan Hukumar KNARDA.
kafin ba shi wannan mukami , Dakta Kurawa shi ne Babban Sakataren gwamnan Kano wato (PPS) .
4. Dr. Tukur Dayyabu Minjibir, Manajan Daraktan Kamfanin Samar da Taki na Kano (KASCO).
5. Hussain Sarki Aliyu Madobi, Manajan Darakta na Cigaban aiyuka a Kano wato (SKP)
6. Sadiq Kura Muhammad, Manajan Darakta na gidan Zoo Kano (ZGK)
7. Injiniya Sani Bala, Manajan Daraktan Hukumar samar da wutar Lantarki a Karkara (REB)
8. Shamwilu Gezawa, hukumar samar da ruwan sha da tsaftar muhalli ta jihar Kano (RUWASA)
9. Alh. Tukur Bala Sagagi, Manajan Darakta na hukumar yawon bude ido ta jihar Kano
10. Alh. Yahaya Muhammad Idris Manajan Daraktan Kamfanin dab’i na Jihar Kano
11. Adamu Yahaya, Mataimakin Manajin Darakta (DMD), Kamfanin dab’i na Kano
12. Abba El-mustapha, Sakataren zartarwa na Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano
13. Dr. Muhammad S. Khalil, Babban Sakatare na Hukumar Kula da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano (KN-WECCMA).
14. Dr. Dahir M. Hashim, Kodineta na Hukumar Kula da Sauyin yanayi ta Jihar Kano (KN-WECCMA).
Sanarwar na umartar Dukkanin wadanda aka nada dasu karbi ragamar aikin da aka dora musu nan take