Mambobin kwamitin gudanarwa (NWC)na jam’iyyar APC ta ƙasa zasu sa labule da gwamnonin jam’iyyar yau Laraba, 19 ga watan Yuli, 2023 a birnin Abuja.
NWC zata gana da gwamnonin ne a wani yunƙuri na neman goyom baya daga manyan masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC bayan murabus ɗin Abdullahi Adamu.
Wannan taro na zuwa ne awanni 48 kacal bayan mataimakin shugaban APC na shiyyar arewa, Abubakar Kyari, ya karbi ragamar jam’iyya a matsayin muƙaddashin shugababa.
Hakan ta faru ne bayan shugaban APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, da sakatare na ƙasa, Iyiola Omisore sun yi murabus daga kan muƙamansu.
A wurin taron da NWC ya gudanar ranar Litinin, an cimma matsayar zaama da masu ruwa da tsaki kan abubuwan da ke faruwa a cikin gida