Rabon Tallafi, Tinibu ya gana da Ganduje da wasu jigajigai

A daren Larabar da ta gabata 19 ga watan Yuli, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da wasu manyan ƙusoshi domin kammala tsare-tsaren yadda za a gudanar da rabon kayan tallafin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.

Shugaban ya gana da mataimakinsa, Kashim Shettima, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da wasu gwamnonin jihohin ƙasar nan.

Tinubu na ci gaba da tattaunawar ne da manyan jiga-jigai kan yadda za a farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan wanda ya shiga wani hali a dalilin cire tallafin man fetur da aka yi.

A dalilin hakan ne shugaban ƙasa da mataimakinsa Sanata Kashim Shettima sun gana da shugaban majalisar dattawa da wasu gwamnoni da suka haɗa da na jihohin Imo, Kwara, Legas da Ogun, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments