Hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS ta bayyana cewa shugaban hukumar EFCC da aka dakatar AbdulRasheed Bawa, yana hannunta domin amsa wasu tambayoyi.
Hukumar ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na twitter.
Sakon wanda jami’in hulda da jama’a na rundunar, Peter Afunanya ya fitar ya ce an gayyaci Bawa ne domin gudanar da bincike kan wasu lamurra da suka shafe shi.
Hakan na zuwa ne sa’o’i kadan bayan shugaban kasa Asiwaju Bola Ahemd Tinubu ya dakatar da shugaban na EFCC.
Wata sanarwa da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin Tarayya a jiya ta ce Tinibu ya ɗauki matakin dakatar da Bawa ne domin bayar da damar gudanar da bincike kan wasu manya-manyan zarge-zargen da ke kan shi.
Sanarwar, wadda ta samu sa hannun daraktan yaɗa labarai na ofishin sakataren gwamnatin Tarayya, ta ce an bai wa Abdurrasheed Bawa umurnin miƙa aiki ga daraktan gudanarwa na hukumar, wanda zai kula da yadda za a gudanar da binciken.