Cibiyar nazarin harkokin diflomasiyya ta Venancio de Moura (ADVM) a kasar Angola ta sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tare da kwalejin Confucius na jami’ar Agostinho Neto (UAN) dake kasar Angola, don kafa wani aji na koyar da harshen Sinanci da al’adun kasar Sin.
Cibiyar ADVM za ta kasance jami’ar Angola ta biyu, bayan UAN da za ta rika koyar da kwasa-kwasan Sinanci a hukumance tare da tallafin cibiyar Confucius da ke Angola.
A jawabinsa yayin bikin sanya hannun, babban daraktan cibiyar ADVM Jose Marcos Barrica, ya bayyana muhimmancin yarjejeniyar, yana mai cewa, ajin zai taka muhimmiyar rawa wajen karfafa dangantakar dake tsakanin al’umomin Angola da Sin.
Shi ma a nasa jawabin yayin bikin, jakadan kasar Sin dake Angola Gong Tao, ya bayyana kyakkyawan fatansa game da yarjejeniyar fahimtar juna, inda ya bayyana cewa, za ta ba da wani sabon kuzari ga hadin gwiwar al’adu tsakanin kasashen Sin da Angola