Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf da aka fi Sani da Abba Gida-gida yace a yanzu haka gwamnatin sa bata da wani shiri a kasa na soke masarautu biyar dake fadin jihar nan
Tun a jiya ne dai Rahotanni suka cika kafafen sadarwa masu nuni da cewa gwamnatin ta shirya gabatar da kuduri gaban Majalisa akan soke masarautun.
Jaridar solace bace ta rubuto cewa jagoran jam’iyar NNPP kuma Madugun Darikar kwankwasiya Engr Dacta Rabiu Musa Kwankwaso a zantawar sa da manema labarai yace gwamnatin Abba zata duba yadda aka bi aka kafa sabbin masarautun