Rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar Rivers ta tabbatar da kama dan majalisar tarayya na jihar Rivers, Dakta Chinyere Igwe, dauke da makuden kudaden kasar waje da ba a bayyana adadinsu ba.
Mai magana da yawun rundunar, Grace Iringe-Koko ta tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar The Punch.
Tace an kama Igwe, wanda ke wakiltar mazabar Port Harcourt na 2 a majalisar tarayya, a ranar Juma’a da safe a Aba Road a Port Harcourt
Dan majalisar tarayya na jihar Rivers, Chinyere Igwe da aka kama da kudin kasar waje.