Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta sanar da cewa ta tanadi jami’ai 200 domin yaki da masu siyen kuri’u a guraren gudanar da zabuka
Hukumar ta bayyana hakan ne ta bakin shugaban ta dake rike da shiyar Kano katsina da Jigawa Malam. Farouk Dogon daji a zantawar sa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN
Dogon Daji yace hakan na cikin kudire-kudiren hukumar na ganin ta yaki cin hanci da rashawa ta kowacce fuska.
Cikin Lafazin sa yace “mun tanadi jami’ai 50 a Kano da 50 a katsina da kuma 50 a Jigawa, wadanda zasu rika kewayen dan kama duk wanda a ka gani yana siyen kuri’u