Yanzu-yanzu INEC ta raba lambobin da za’a iya tuntubar ta a ranar zabe
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC a kokarin ta na yaki da labaran karya ta samar da lambar da za’a iya kiran su a waya domin sanin mai yake gudana a hukumar
Hukumar ta bayyana hakan ne ta bakin shugaban sashin yada labarai da wayar da kan masu zabe na hukumar Festus Okoye
Yace dan samun sahihan labarin halin da ake ciki a lokacin tattara kuri’u za’a iya kiran wadannan lambobin 4623 kuma a take za’a baka amsa