Matsin tattalin arziki a Najeriya ya tursasa wa wasu da dama sauya tsarin rayuwarsu game da yin aure.
Tun wuraren shekarar 2019 ne matsalar matsin tattalin arziki ta ta’azzara a Najeriya, da ta haɗa da hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar, lamarin da ya yi ƙamari a 2021 saboda tasirin annobar cutar korona da na yaƙin Ukraine da Rasha da ke shafar ƙasashen duniya ciki har da Najeriya.
Hussaini Mukhtar, wani matashi a jihar Kano da ke arewacin kasar, na daga cikin mutanen da ke jin tasiri da raɗaɗin matsin tattalin arziki ta yadda hakan ya tilasta masa haƙura da wasu abubuwa na jin dadin rayuwa.
“Rayuwa ta yi wahala sosai, tsada da wahalhalu sun ƙaru saboda rashin kudi da tashin farashin kayayyaki da kullum ake ciki” inji Husaini
Sai dai a nata bangaren, gwamnatin ta sha cewar tana iyaka kokarinta domin ganin abubuwa sun kyautatu a fadin kasar.
Matasa dai sunata kokarin rage burika da dama duba da halin da al’umma ke ciki na matsi a fadin kasar.
To koya abun yake ga yan mata?
Ku aje mana sakon ra’ayoyinku.