Daga Walid Hari.
AC Milan na sha’awar sayen dan wasan Chelsea kuma dan wasan tsakiya a Ingila mai shekara 26 Ruben Loftus-Cheek wanda kwantiraginsa da kungiyar zai ci gaba har shekarar 2024. (Calciomercato – in Italian)
Chelsea na gab da kulla yarjejeniya domin nada babban mai daukar ma’aikata na Southampton Joe Shields a matsayin daraktan daukar ma’aikata. (Guardian)
Manchester City ta fada wa kungiyoyi da dama har da Bayern Munich da Inter Milan da suka nemi bayani kan dan wasa Nathan Ake cewa ba za su sayar da matashin mai shekara 27 ba a watan Janairu. (90 Min)
Rahotanni na cewa Manchester United ta zafafa neman mai tsaron ragar Benfica Odysseas Vlachodimos kuma a shirye suke su saye dan wasan dan shekara 28 wanda Leicester City take nema. (Sportime – in Greek)
Brentford ta bude tattaunawa game da sabuwar kwangila da dan wasan Ingila mai shekara 26 Ivan Toney wanda aka danganta da Tottenham. (Football).