Shugaba Putin na da kwarin gwiwar ci gaba da yakin duk kuwa koma-bayan da dakarunsa ke samu.
Daga Walid Hari.
Akwai shakku game da maganganun da ke cewa shugaba Putin na fuskantar matsin lamba, a mamayar da yake yi wa Ukraine wadda ya kira ‘Atisayen soji na musamman’ na fuskantar koma baya, dalilin da ya sa a ‘yan kwanankin shugaban ya sake shiri da fasalin yakin.
Kawo yanzu dai yakin na kusantar wata takwas da fara shi, kuma babu alamun kawo karshensa nan kusa. Rasha dai ta bayyana asarar sojoji masu yawa a yakin, inda a ‘yan makonnin baya-bayan nan take rasa iko da wasu yankuna da a baya ke hannunta.
Idan muka koma abin da ke zuciya Putin, shin yana ganin hakan a matsayin wani gazawa a gare shi, kuma yana kallon matakinsa na mamayar Ukraine a matsayin kuskure?
Masana da dama suna da shakku game da haka saboda a ganinsu kasar ba ta da isassun makaman da za ta iya yin hakan”, in ji Mista Remchukov.
Sai dai Putin ya raina karfin sojin Ukraine da al’umar kasar inji Masana da dama na siyasar duniya.