Daga Sadik Lamin Hassan
Gwamnatin tarayya tace gyaran hanyar Abuja-Kaduna-Kano da ake yi ya tsaya a dalilin barazanar da ake fuskanta na rashin tsaro a yankin.
Karamin Ministan ayyuka da gidaje, Umar Ibrahim El-Yakub yana mai wannan bayani yayin da ya duba wani aikin titi a Kaduna.
Hon. Umar Ibrahim El-Yakub yace an tsaida aikin bayan harin da aka kai wa jirgin kasan Abuja-Kaduna a watan Maris, aka yi gaba da wasu fasinjoji.
Rahoton yace Ministan ya fitar da jawabi a karshen makon da ya gabata ta bakin Darektansa na yada labarai da hulda da jama’a, Blessing Lere-Adams.
Blessing Lere-Adams tace akasin abin da mutane ke fada cewa an yi watsi da aikin, ba haka lamarin yake ba, an dakata da aikin ne kuma za a cigaba.
A cewar Umar Ibrahim El-Yakub, aikin ya kai matakin da za a yabawa gwamnati, ya kuma tabbatar da cewa ‘yan kwangila za su kammala ginin titin a lokacin da aka tsara.
“Muna sa ran bangare na biyu da na uku na hanyar za su kammala daga yanzu zuwa farkon shekarar badi.
Amma bangare na farko zai dauki fiye da wannan lokaci, saboda dalilan da suka bayyana a zahiri.
‘Dan kwangila yana aiki a sauran bangarorin hanyar a lokaci daya kafin ‘yan ta’adda su kai harin jirgin kasa
Kuma an yi fiye da 50% na aikin a sashen farko kafin ‘dan kwangilar ya tsaida aiki saboda rashin tsaro.”
Darektar ma’aikar ayyuka da gidajen tace ba da dadewa ba za a cigaba da aikin wannan titi na Abuja-Kaduna-Kano domin an samu tsaro a yanzu.
Ministan ya kuma bayyana cewa aikin yana cigaba da tafiya a sauran bangarorin titin.