Yan sanda sun Damko a matashin da ya kashe budurwarsa ya cika wandon sa da iska

A bayalsa Yan sanda sun sami nasarar kame wanda ya kashe budurwarsa:

Hukumar  ‘yan sanda ta kasa reshen jihar Bayelsa, sun tabbatar da kama wanda  ake zargin ya kashe Budurwar sa mai shekaru 22.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Asinim Butswat, shine  ya tabbatar da faruwar lamarin,

Mutumin da ake zargin ya aikata laifin kisa, mai suna Arepamowei Koru, dan kabilar Ogobiri a karamar hukumar Sagbama ta jihar Bayelsa, ya lakada wa budurwarsa ‘yar shekara 22, Miss Toma Serve-god Angolo dukan tiyata da yayi sanadiyar mutuwar ta har Lahira.

Tun da fari dai hatsaniya ta kaure  tsakanin masoyan biyu wanda ya kai ga Saurayin ya aike da masoyiyar tasa har Lahira, lamarin da yasa ‘yar uwar wadda aka kashe ɗin ta yi ihu na neman temako tare da rike Kuro dan kada ya tsere.

Masoyan dake zaune ne a unguwa É—aya kafin faruwar lamarin.

Mazauna unguwar sun shaidawa manema labarai cewa, masoyan biyu sun zauna tare ba tare da an samu wani sabani a tsakanin su ba, kafin Æ´ar karamar rashin jituwar ta shiga tsakanin su a ranar Talata da ta kai ga kisa.

A cewarsu, mutumin ya yi mata duka a wani bangare na jiki mai hadari wanda ya kai ga zubar jini kafin mutuwar yarinyar.

“Sun kuma ce taimakon ‘yar uwar marigayiyar ce ta samu nasarar cafke mai laifin kafin ta sanar da ‘yan sanda domin su kama shi.

Mahaifin marigayiyar, Mista Servegod Angolo, ya garzaya da ita zuwa Asibitin Tarayya da ke Yenagoa, sai dai kafin isar su Rai yayi halin sa

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments