Daga Ibrahim sani gama
Kungiyar matasan karamar hukumar ungogo sun koka sakamakon karancin sabbin kudade a injinan cirar kudi na (ATM) a Bankuna da kuma,cinkoson alumma a nan jihar kano.
Shugaban kungiyar Alh Bashir Tukur BTD ne yayi wannan koken a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa dake gadar rimin kebe.
Bashir BTD ya bayyana cewa,ya kamata Gwaamnati ta kara wa,adin da ta sanya na dakatar kabar tsuffin kudade a Bankuna duba da yadda alumma suke shan bakar wuya wajen kai kudadensu bankunansu don ajiyewa da wandanda suka Dade suna boye da kudaden da suke kasuwanci da su a kusa da su,Wanda wannan ba karamin kalubale bane.
Yace,sakamakon cinkoson da ake samu mutane da yawa sun rufe kasuwancinsu da kantinansu da masu kananan sana,oi,musamman a cikin unguwanni,wasu kuma basa karbar tsofaffin kudade duk da cewa wa,adin daina karbar kudin bai cika ba,saboda babu isassun kudaden ko da a masu sana,ar nan ta POS Wanda idon aka tafi a haka ba karamar matsala bace a cikin alumma saboda mutane da dama suna cikin matsala,duk da wahalar da suke sha wajen samo kudaden sannan a ki karbarsu.
Duba da haka,shugaban kungiyar ya ga da akwai bukatar yin kira ga Gwamnati da Gwamnan Babban Bankin NajeriyaMr.Goodwin Emefele da su taimaka wajen kara wannan wa,adin domin alumma su ji dadin ajiye kudadensu cikin sauki batare da sun sha wata wahala ba.
Haka kuma,ya yabawa majalisar Dattijan kasar nan bisa bukatar da suka yi wajen ganin babban Bankin ya kara lokaci ta yadda alumma za su samu saukin alamuransu ,musamman kananan yankasuwa da masu saye da siyarwa a cikin lungu da sako na cikin birni da karkara wadanda sune suke kusa da alumma.
Ya kuma yi kira ga alummar Najeriya da su taimaka da addu,oin samun sauki daga wajen Allah subahanahu wata,ala saboda halin da alumma suka samu Kansu a ciki yana bukatar adduoi da tamakekeniya a tsakanin juna Wanda yin hakan ba karamar nasara bace.