A wani mataki na nuna goyon baya ga tsarin dimokaradiyya a kasar nan, gwamnatin Amurka ta sanya takunkumin bulaguro ga mutanen da ke da hannu wajen yin zagon kasa ga dimokradiyyar Najeriya
Shugaba Joe Biden na kasar Amurka shine ya bayyana hakan inda yace “A yau ina mai shelar hana bisa ga masu yin kafar ungulu ga dimokaradiyyar Najeriya, saboda in tallafa ma zabukan Najeriya da ke tafe. Amurka tana goyon bayan burin Najeriya na yaki da cin hanci da rashawa da kuma karfafa dimokradiyya da bin doka da oda.”
Sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ne ya fadi haka yau Laraba 25 ga watan Janairu a wata sanarwa ta musamman.