Rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar Sakkwato ta kama wani mutumi mai suna Nasiru Idris ɗauke da Katunan Zaɓe (PVC) guda 101.
Nasuru wanda ya fito daga yankin ƙaramar hukumar Sabon Birni a iya cewa ya biyewa son zuciyar sane.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Hussain Gumel, shi ne ya bayyana haka yayin zantawar sa da manema labarai a yau ranar Alhamis.
A cewarsa bayan wata ɗaya zasu miƙa ragowar katunan ga hukumar zaɓe INEC idan masu su basu karɓa ba