Hukumar kula da Zirga-zirga Ababen Hawa ta jiha KAROTA ta sami nasarar cafke cafke wasu matasa biyu da zargin sace wayar Fasinja a cikin Baburin Adaidaita Sahu.
Mai magana da yawun hukumar nabilisi abubakar shine ya tabbatarwa da jaridar aksammedia tabbacin afkuwar lamarin
Waɗanda ake zargi da satar wayar sun haɗa da; Ibrahim Sale Rijiyar Lemo da Abubakar Salisu Zoo Road bisa zargin sace wayar fasinjan Adaidaita Sahu Hassan Muhammad Sani
Hassan Muhammad ya ce lokacin da ya tsayar da su ya neme su kai shi Bata daga shatale-talen gatar Dangi bayan sun ɗauke masa wayarsa sai suka ce ba inda ya bayyana za su je ba
Bayan da Hukumar KAROTA ta sami nasarar cafke matasan, sun bayyana mata cewa sun shafe fiye da shekara guda suna aikata wannan mummunar ta’adar ta ɗaukar Fasinja a cikin Baburin Adaidaita Sahu mai lambar KAROTA KRY 1539
Hassan Muhammad ya kara da cewa bayan da ya sauka ne sai ya fahimci sun ɗauke masa, a inda ya nemi taimakon jami’an KAROTA da ke aiki a wannan wuri.
Hukumar ta miƙa su hannun Rundunar ‘Yansanda ta jihar Kano domin ta faɗaɗa bincike tare da gurfanar da su a gaban Shari’a
Lokacin da Hukumar ta kama su ta sami wayoyi iri daban-daban a hannunsu tare da nau’in kayan shaye-shaye
Shugaban Hukumar ta KAROTA Hon. Baffa Babba Ɗan’agundi ya ƙara kira ga al’umma da su cigaba da sa ido a duk lokacin da za su hau Baburin Adaidaita Sahu tare da lura da Koriyar lambar jiki da irin mutanen da suke ciki domin gujewa faɗawa hannun ɓata-gari in