Kwamishinan yan sanda na jihar Kano, CP Muhamud Dauda ya bayyana tanadin da rundunar sa ta yi na jami’an yan sanda 18,748 domin aikin bayar da tsaro a lungu da sako na jihar Kano.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN.
Yace rundunar sa da wasu hukumomin tsaro tuni sun tanadi kayayyakin kwantar da tarzoma kuma an kasafta su ga akwatina 11, 222 dake mazabu 484 a kananan hukumomi 44 na jihar Kano.
Kazalika yace tuni an bayar da oda ga kowanna Baturan yan sanda dake fadin jihar Kano.