Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta sanar da shirin tsunduma yajin aikin gargadi na kwanaki 7 don tilasta wa gwamnatin kasar magance matsalar karancin takardun Naira da man fetur wanda ya jefa jama’a a halin tsaka mai wuya.
Wata sanarwa da NLC ta fitar yau Talata dauke da sa hannun shugabanta Joe Ajaero da kuma babban sakataren kungiyar Emmanuel Ugboaja ta bukaci gwamnatin kasar ta gaggauta kawo karshen matsalar da ake ciki.
Matakin tsunduma yajin aikin kamar yadda sanarwar ta bayyana, ya biyo bayan taron kolin da NLC ta gudanar a jiya Litinin wanda ya kai ga tsunduma yajin aikin gargadin don tilasta wa gwamnati daukar matakin magance matsalar.
A cewar NLC, gaza wadata al’umma da takardun kudin Nairar walau sabbi ko tsaffi ya jefa jama’a cikin matsin rayuwa yayin da a bangaren karancin fetur ya sake tsawwala matsin rayuwar da ‘yan Najeriyar ke fama da shi.
Sanarwar ta yi barazanar tsunduma yajin aikin na tsawon kwanaki 7 da nufin tilasta wa gwamnati wadata kasar da takardun Naira kamar yadda ake a baya.
Duk da matakin CBN na sahale ci gaba da amfani da tsaffin kudin da ya dakatar a baya, sakamakon hukuncin Kotun Koli, wasu majiyoyi sun ce har yanzu da dama daga cikin ‘yan Najeriya sun gaza samun takardun kudin a hannun su