Rasha ta amince ta tsawaita yarjejeniyar fitar da hatsi daga kasar Ukraine ta kan tekun Black Sea, a daidai lokacin da zango na biyu na wannan yarjejeniya ke gab da karewa.
Waadin yarjejeniyar zai kare ne a ranar 18 ga wannan wata na Maris amma Rasha ta ce, ta amince ta tsawaita ta da wasu karin kwanaki 60 masu zuwa.
Majalisar Dinkin Duniya da Turkiya ne suka jagoranci cimma yarjeniyar fitar da hatsin a tashin farko tun a cikin watan Yulin bara domin tabbatar da safarar kayan abinci cikin aminci, a daidai lokacin da kasashen biyu ke yakar juna.
A cikin watan Nuwamban da ya gabata ne, aka fara tsawaita yarjejejiya da kwanaki 120, inda kawo yanzu aka yi safarar kimanin tan miliyan 23 na hatsi daga Ukraine ta kan tekun Black Sea duk da yakin da ake fama da shi.
Sai dai gwamnatin Ukraine ta bakin Ministan Kula da Kayayyakin More Rayuwa a kasar, Oleksandr Kubrakov ya bayyana cewa, matakin Rasha na tsawaita yarjejeniyar ya saba wa takardun da Turkiya da Majalisar Dinkin Duniya suka rattaba wa hannu.
Ministan ya ce, suna dakon Majalisar Dinkin Duniya da Turkiya su tsonma baki a matsayinsu na wadanda suka jagoranci cimma yarjejeniyar tun asali, domin kuwa, kamata ya yi Rasha ta tsawaita yarjejeniyar da kwanaki 120 a cewarsa.