Sama da ‘yan Najeriya 11,000 daga yankin Neja Delta mai arzikin man fetur ne suka shigar da karar kamfanin Shell SHEL.L a gaban babbar kotun birnin Landan, mataki na baya-bayan nan a shari’ar da za ta sa a ga ko wasu ‘yan kasa na ketare na iya neman hakkinsu.
A shekarar 2021, kotun kolin kasar Birtaniya ta amince wa wasu manoma da masunta 42,500 ‘yan Najeriya da su kai karar kamfanin Shell a kotunan Ingila bayan shafe shekaru da dama ana zubar da mai da ya gurbata kasa da ruwan karkashin kasa.
Alkalan sun ce a lokacin akwai wata hujjar cewa Shell, daya daga cikin manyan kamfanonin samar da makamashi na duniya ne ke da alhakin hakan, saboda yana da iko sosai kan reshensa na Najeriya SPDC.
A ranar Alhamis din nan ne wani ‘dan kamfanin lauyoyi na kasar Birtaniya, Leigh Day, ya ce ya shigar da kara a madadin mutane 11,317 da cibiyoyi 17 da suka hada da coci-coci da makarantu daga al’ummar Ogale da ke yankin Neja Delta domin biyan diyya saboda asarar rayuka da barnar da kamfanin Shell ya yi.
Leigh Day ya ce wannan ikirarin na Ogale ya cancanci dubawa. Ya kara da cewa ‘yan kabilar Bille ne suka kawo a shekarar 2015. Hakan ya sa adadin mutanen kauyen da ke neman diyya daga Shell ya karu zuwa 13,652.
Ikirarin ya ce malalar mai da ta biyo bayan ayyukan kamfanin Shell a yankin Neja Delta ta lalata gonaki da gurbata ruwan sha da kuma illa ga rayuwar jama’a.
Mataki na gaba a cikin shari’ar shine a kafa shari’ar gudanar da shari’ar a cikin bazara na 2023, gabanin cikakken shari’ar da ake iya yi a shekara mai zuwa,” in ji Leigh Day a cikin wata sanarwa.
Mai magana da yawun Shell ya ce yawancin malalar da ke da alaka da ikirarin Ogale da Bille na faruwa ne sakamakon miyagun ayyukan wasu mutane, ciki har da masu fasa bututun mai amma SPDC za ta ci gaba da tsaftace wuraren da abin ya shafa.