China zata kaddamar da Na’urar Wukong mai kwakwalwa

A yanzu haka shiri ya yi Nisa na kaddamar da sabuwar Na’urar Quantum da kasar China ke kokarin kaddamar wa kasancewar an gabatar da kananan na’urorin chip da zasu yj aiki a jikin kwamfiyutar ta Quantum.

China a karon farko, na yunkurin samar da na’ura mai Kwakwalwa da aka yi wa suna Wukong wadda aka gwada ta a halin yanzu

Jia Zhilong, mataimakin daraktan cibiyar binciken ayyukan injiniyanci da tsarin Na’ura mai Kwak walwalar ta Quantum a lardin Anhui, ya ce a karshen shekarar da ta gabata ne aka samar da kanana na’urorin chip na Quantum da aka sanyawa Wukong, inda a yanzu haka suke aikin tantancewa da cire kurakurai a cikin sabuwar Na’urar kumfyutar.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments