Badaqalar N89 trillion: Hon. Gudaji Fa Ya Yi Tambaya
Ni ma dai da kamar Jafar Jafar da sauran wasu yan Nigeria da ke ganin wadannan kudin zai yi wuya ace Nigeria ta mallake su har an boye su cikin wani account na sirri ko kuma ma ace an sace su.
Amman bayan da na kalli live nterview da su Jafar Jafar, Abba Hikima, Bulama Bukarti da Nasiru Zango su ka yi da Hon. Gudaji Kazaure, gaskiya tunani ya chanza. Dalili na kuwa shine irin hujjojin da Hon. Gudaji Kazaure ya gabatar ma su Jafar Jafar. Hujjojin da kuma a lokacin ba wanda ya musanta su daga cikin su.
Misali, Jafar Jafar ya yi ma Hon. Gudaji Kazaure tambaya kamar haka:
“A na maganar gaba daya banking assets na Nigeria, da kudin da ke cikin banki, da motocin su da gine-ginen su da kome na su bai kai N50trillion ba. Ka na maganar ka ga wani account da ke da N89 trillion……..ta ya aka yi haka?”
Amsar Hon. Gudaji Kazaure:
“Alhamdulillahi. Kudin nan su na taruwa ne ba wanda ya sani. Ita da kan ta Central Bank ta ce ta ranta ma bankuna N23 trillion. Daya kenan. Na biyu, total equity (Watau dukkan dukiyar da Central Bank ta mallaka) na Central bank is N0.3 trillion….amman sun rantawa bankuna N23 trillion. Ina su ka same su? Daya kenan. Na biyu, sun rantawa Federal government N13 trillion. Kudin nan da aka Kai Senate aka ce ayi approving (Na ji interview ta BBC da Sen Babba Kaita on the issue), da Senate su ka tambaya ina aka ranto wadannan kudin? Aka ce daga Central Bank. Kusan N22 trillion….idan har Central Bank za ta ranta ma bankuna N23 trillion kuma ta ranta ma federal government N22 trillion in ka hada zai ba ka N45 trillion… (ina aka samo su)”
Idan mutun mutun ya hada kudaden da Central Bank ta ba da rance, kamar yadda Gudaji Kazaure ya lissafa:
1. N23 trillion to banks
2. N13 trillion to Federal government
3. N22 trillion to Federal government (spent without appropriation)
Total is N58 trillion.
Idan CBN da arzikin ta bai wuce N0.3 trillion ba, ina ta samu N63 trillion da ta ba da rance?