NNPCL ta biyo hanyar da za’a daina siyar da litar Man fetur sama da 185

Hukumar NNPCL ta kasa ta dauki gabarar rarraba Man fetur zuwa kowanna gidan Mai na yan kasuwa dake fadin kasar nan a shirin ta na dawo da siyar da litar Mai akan farashi da ta ambata na 185.

Shugaban kungiyar dillalan Mai ta kasa Chinedu Okoronkwo, sun cimma matsayar ne bayan taron tattauna wa da suka gudanar da hukumar NNPCL kuma ya ce suna Maraba da wannan matakin na hukumar NNPCL din ta kasa.

Da yake jawabi ga kamfanin dillancin labarai na kasa Mista Okoronkwo ya mambobin kungiyar su zasu rika yin lodi daga kowanna depot na NNPCL da Mrs dake fadin kasar nan.

A karshe ya shawarci manbobin su da su tanadi kawunan POS domin bunkasa harkokin su duba da an koma tsarin takaita yawo ko tara takardun kudi

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments