A ranar bakwai ga wata, a Yamai, babban birnin kasar Nijar, an dauki haramin babban dandalin kasa da kasa na tarayyar Turai da kasar Nijar, wadanda aka ma taken BUSINESS FORUM NIGER-EU karo na farko, wanda aka bude a babban zauren taro kasa da kasa na Mahatma Gandhi da ke birnin Yamai. Shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum ya bude bikin wannan dandali.
A cikin biyu daga ranar 7 zuwa 8 ga watan Fabrairun shekarar nan, a karkashin jagorancin ma aikatar kasuwanci da tawagar tarayyar Turai, zai baiwa mahalarta dandalin da suka fito daga kasashen Tarayyar Turai kamarsu Faransa, Jamus, Denmark, Holland, Belgium, Italiya, Birtaniya, Portugal, Switzeland da sauransu tare da kasar Nijar da su tattauna da yin musanya a fannoni daban daban, da kuma duba babin dangantakar bangarorin biyu da makomarta. Haka kuma, babban burin wannan dandali shi ne karfafa huldar tattalin arziki tsakanin tarayyar Turai da Nijar, da kuma gabatar da damammakin zuba jari, da ake baiwa masu zuba jari na Nijar, na shiyyar Afrika da Turai.
A yayin wannan dandali, wakilan tarayyar Turai za su kai ziyara a wuraren da aka gudanar da manyan ayyuka cikin tsarin sabbin dubaru na Global Gateway na tarayyar Turai. Hadin gwiwar aiki na abokan huldar tarayyar Turai dake ingiza kokari a Nijar, musamman ma kan gine-ginen ababen more rayuwa a cikin muhimman fannoni kamar makamashi, samar da ruwa masu tsafta da kuma ilimi. Haka kuma, wannan dandalin tarayyar Turai da Nijar, yana daya daga cikin manyan taruka na bunkasa bangaren masu zaman kansu, kyautata yanayin kasuwanci da hada-hada a Nijar, da kuma ingiza ci gaban tattalin arziki da na jama’a na kasar Nijar. Haka zalika, aikin noma, kiwo, sabbin makamashi, gine-gine, sabbin fasahohin zamani NTIC da aikin hannu su ne kuma fannonin da za a fifitawa a yayin wannan haduwar ta kwanaki biyu.
A dunkule kusan mahalarta 700 ake sa ran za su zo daga cikin fiye de kamfanoni 400 na tarayyar Turai, Nijar da shiyyar Afrika, tare da masana da kwararru fiye de 50 za su halarci taruka daban daban da sauransu