Yan Majalisar tarayya sun cikakken jawabi akan Biliyan 70 din da suka ware wa kan su

Ƴan Majalisar wakilai sun fara mayar da martani dangane da sukar da ake musu na warewa kansu Naira biliyan 70 daga cikin Naira biliyan 500 da suka amince wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kashe, wajen ba wa ‘yan kasar tallafin rage radadin janye tallafin man fetur da gwamnatinsa ta yi.

Da dama daga cikin ‘yan NajeriyaA na ganin matakin da ƴan majalisar suka dauka ya nuna yadda suka fi fifita bukatunsu a kan na jama’a, wadanda dama ke cikin wahala.

Sai dai a cewar wasu daga cikin ‘yan Majalisar irin su Injiniya Sani Bala Tsanyawa daga jihar Kano, sabanin yadda mutane ke cewa su za a raba wa kuɗin, za a yi amfani da su ne wajen yin gyare-gyare a majalisar, da biyan albashin ma’aikata masu musu hidima, da sauran bangarorin majalisar.

Yayin wata hira da yayi da manema labarai , dan majalisar ya ce: ”An ware wa wasu bangarori da dama nasu kudaden, me ya sa sai majalisa kadai za a sanya wa ido?”

Akwai yan majalisa 469 ciki har da yan majalisar dattawa, kowannensu kuma zai dauki ma’aikata guda biyar, ka ga ke nan sai ka ninka wannan adadi na 469 sau biyar, dukkansu kuma za a dauke su aiki ne daidai da matakin gwamnatin tarayya, kuma sai ka biya su alawus, sai ka kula da wajen zamansu a kwana 28 na farko, don haka da wannan kudi za a yi amfani wajen yin duk wannan dawainiya,” in ji shi.

Ya yi bayanin cewa Naira biliyan 70 din da suka ware wa kansu na cikin wata Naira biliyan 300 da Shugaba Tinubu ya nema ne tun da farko, ba wai cikin biliyan 500 din da aka kebe domin rage wa talakawan kasar radadin janye tallafin mai ba.

Kungyoyin masu fafutuka a Najeriya sun yi Allah-wadai da matakin yan majalisar, da suke kallo a matsayin harambe da fifita kai.

Kungiyar SERAP ta lashi takobin ruga wa gaban kotu, domin kalubalantar matakin yan majalisar idan har ba su janye ba.

Sai dai a cewar Injiniya Sani Bala Tsanyawa, ware irin wadannan kudade domin tafiyar da harkokin majalisa ba sabon abu ba ne, domin kuwa yana faruwa a kowa ce kasa, kamar yadda ya ce.

”Najeriya ba kasa ba ce da ake zaune kara zube, duk abin da aka yi an yi shi ne bisa doka, kuma ba wani sabon abu ba ne,” in ji shi.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments