Peter Obi ya yi magana kan shirin Shugaba Tinubu na raba tallafin N8,000 ga iyalai 12m har na tsawon wata shida
Obi ya bayyana cewa tallafin N8,000 ya yi kaɗan ya rage raɗaɗin da ƴan Najeriya suka samu kansu a ciki a dalilin tsige tallafin man fetur
Sai dai, tsohon gwamnan na jihar Anambra ya bayyana cewa ya gayawa ƴan Najeriya cewa su shiga cikin tsarin domin samun tallafin