Kungiyar kasuwar Abinci ta Dawanau dake karamar hukumar Dawakin Tofa,ta bayyana gamsuwarta bisa tsarin da Babban Bakin Najeriya (CBN)ya bijiro da shi a kasar nan domin takaita zirga zirgar kudade a hannun alummar kasar nan.
Sakataren kungiyar kuma,Garkuwar matasan Arewacin Najeriya, Kwamared Rabiu Abubakar Tumfafi ne,ya sanar da haka a lokacin da yake zantawa manema labarai anan jihar kano.
Rabiu Abubakar Tumfafi,yace,takaita zirga_zirgar kudaden a hannun alumma za ta ragu saboda wannan tsari da Babban Bankin Najeriya ya fito da shi zai taimakawa yankasuwa wajen aiwatar da kasuwancinsu na yau da kullum.
Garkuwar matasan ya kara da cewa,ta fannin yawo da makudan kudade da wasu daga cikin alumma suke yi kodaushe zai zama tarihi duba da hada hadar kasuwancin da suke yi,musamman masu zuwa wasu jihohin Najeriya domin siyo kayayyakin da suke kasuwancinsu,ko don kaucewa barayi da sauran wata fargaba da suke tunanin za ta iya afkuwa akan hanyoyin da suke zuwa fatauci.
Rabiu Tumfafi ya ja hankalin matasan Arewacin Najeriya da su kaucewa shiga cikin bangar siyasa, musamman sakamakon yadda lokacin Babban zabe yake karatowa ,Wanda ya jaddada cewa,kamata yayi matasan su yi amfani da wannan dama,wajen zaben shugabanni nagari da za su taimakawa rayuwarsu da alummar kasar nan, musamman Daliban da suka kammala karatu basu samu ayyukan yi ba da bijiro da managartan tsare tsaren inganta rayuwa da farfado da tattalin arziki kasacewar Najeriya ta samu kanta a wani yanayi da yake bukatar matasa su kawo dauki domin sune shugabannin gobe.
Garkuwar ya Kara da cewa,kasancewarsa garkuwar matasan Arewacin Najeriya, ya ga dacewar amfani da wannan dama da Allah subahanahu wata,ala ya Dora masa nauyi wajen wayarwa matasa kawunansu da basu shawarwari da za su Nesanta Kansu da shiga cikin bangar siyasa duba da halin da alummar kasar nan, suka samu Kansu a ciki na maysin rayuwa ,Wanda akwai bukatar Jan hankulansu dangane da al,amuran rayuwa na yau da kullum.
Yace,idan matasa suna bari ana amfani da su wajen cin mutuncin wasu abokanan burmin siyasa ta hanyar basu muggun kwayoyi da makamai da sauran abubuwan da za su iya haifar da tarzoma da hargitsi da rikici tsakanin alumma Wanda zai kai ga rasa rayukan alumma.
Daga karshe ya yabawa matasan Arewacin Najeriya, bisa,yadda suka jajirce wajen Neman ilimi saboda da ilimi ne ake samun ci gaba a koina a Duniya.
Ibrahim sani gama pyramid radio.