Ministan Baitulmali da Kudi, Nureddin Nebati ya bayyana cewa Türkiye ta kammala shekarar 2022 a matsayi mafi kyau fiye da sauran kasashen duniya.
Nabati ya bayyana hakan ne a zantawar sa da jaridar star ta kasar, inda yace Turkiyya ta sami tagomashi ta fuskar tattalin arziki da kusan dukkan ma’auni na tattalin arziki, kuma ta ci gaba da samun ci gaba mai karfi
Yace wannan lamari yasa kasar ta kai wani sabon matsayi inda ya jaddada cewa bullo da “Tsarin Tattalin Arziki na Türkiye” wanda ke mai da hankali kan zuba jari, samar da aiyukan yi, samar da kayayyaki da kuma fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, kimanin shekara guda da ta gabata ya ba da gudummawa sosai ga wannan nasarar ta fuskar tattalin arziki.