Daga Ibrahim Abubakar Diso
Gidauniyar ta Umar yusif kashe kobo a wannan karo ta dauki nauyin gudanar da binciken lafiyar Idanun ne ga dinbin al’umma da suka hada maza da mata inda wasu aka basu tabarau wasu magani masu yanar Ido kuma za’a yi musu aiki.
Shugaban Gidauniyar Umar Yusif a jawabin sa yace babu wani dalili na aiwatar da wannan aiki face neman yardar Allah Subhanahu wa Taala.
Kazalika ya ja hankalin mawadata da su kasance masu gudanar da abin da goben su zata inganta wajan kyautata wa al’umma da dukiyar da Allah ya hore musu kuma ya ja hankalin wadanda suka rabauta da wannan tagomashi da subi kaidodin da likitoti suka shimfida musu.
A karshe Suma wadanda suka rabauta da wannan aiki sunyi Addu’a mai tarin yawa ga Gidauniyar da shugaban ta Malam Umar Yusif kashe Kobo.