Kungiyar Dattawan yankasuwar singa na unguwar zango a karamar hukumar ungogo a nan jihar kano,ta nuna mutukar farin cikinta bisa nasarar da Abba kabir Yusuf, ya samu na zamtowa zababben Gwamnan jihar kano.
Shugaban kungiyar Alh. Sammani Mohammad Abdulmuminu,ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa dake kasuwar singa.
Sammani ya taya Abba kabir Yusuf, murna da fatan alheri domin yin wannan nasara da yayi ,Wanda alummar jihar kano suka taka mahimmiyar rawa ta fannin yin addu,oi da ba da gudunmawarsu wajen ganin an samu nasara a zabukan da suka gudana.
Yace,yanzu lokaci yayi da Gwamnatin Abba kabir Yusuf, za ta fara sauke alkawarin da ta dauka a yayin yakin Neman zaben Gwamna Dana yanmajalisu,musamman bangaren harkokin ilimi Wanda shine jigon kawacce alumma a cikin kwanakin Dari na farkon zangon mulkin Gwamna Abba kabir Yusuf.
Alh.sammani, yace,Gwamnatin Abba Gida_Gida,za kuma ta yi duba a fannin harkokin kiwan lafiya da kasuwanci, musamman yadda jihar kano, take cibiyar kasuwanci, za,a kawo managartan tsare tsare da za su inganta rayuwar matasa da yankasuwa,kasancewar alumma sun sha wahala a Gwamnatin da ta gabata.
Yace,hakan ba zai yiyu ba sai alummar jihar kano sun baiwa Gwamnatin Abba kabir Yusuf, cikakken goyan bayan daya kamata musamman addu,oin da za su taimaka wajen cimma nasarar da ake da bukata.
Alh sammani zango,ya sha alwashin cewa,kungiyar yankasuwar Singa, kuma,Dattawan karamar hukumar ungogo a shirye suke wajen ci gaba da baiwa Abba kabir Yusuf, hadin kan daya kamata domin kawo babban ci gaba mai dorewa a kawanne fanni domin ganin alummar jihar kano, sun amfana,musamman wajen sharbar romon dimakaradiyya.
Haka zalika,ya shawarci matasa maza da mata da sauran yankasuwa da su kwantar da hankulansu domin wannan Gwamnati ce,da za ta taimaki alumma da bunkasa harkokin da suka durkushe,musamman lafiya da kasuwanci da ilimi da sufuri da tsaro da sauran al,amuran rayuwar alummar jihar kano.
Daga karshe ya yabawa alummar jihar kano da suka fito,suka kuma, jajirce da ba da gudunmawar da ta kamata domin kawo sauyin Gwamnati,inda yace, insha Allahu alumma za su dara,za kuma su amfana dangane da gudunmawar da suka bayar a zabukan da suka gudana.
Ibrahim sani gama pyramid radio. Don Allah garko ka saka min shi.Nagode da kwarai da gaske.