Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta wallafa cewa ta ware ranakun 29 zuwa 31 na watan Maris a matsayin ranekun da zata mika shedar lashe zabe ga gwamnoni da yan Majalisun jiha da aka gudanar ranar 18 ga wannan wata na Maris
Shugaban sashin bayanai dawayar da ilmantar da masu zabe Mr Festus Okoye shine ya bayyana hakan ga manema labarai.
Yace zasu yi hakan ne bisa doron doka kamar yadda kudin tsarin mulki 72 (1) na hukumar INEC na 2022 ya tanada cewa a mika sakamako ga wanda ya lashe zabe cikin kwanaki 14