LEMUN SHAYI MAI SANYI (ICE TEA)
Kayan hadi:-
•Ganyan shayi
•Suger
•Leman tsami
•Na’a-na’a
•Kanunfari
Yadda Ake Hadawa
– Za’a dafa duka kayan amma banda suger da leman tsami.dafa suger da ruwa.matse leman tsami a kofi ajiye gefe daya.
Tace ganyan shayi da rariya, zuba suger da leman tsami. Saka cikin firijin(Refrigerator) yayi sanyi sosai.
Idan za’a sha saka ganyan na’a-na’a da aka tsinka guda biyar a ciki da leman tsamin da aka yanka akekkewayo a ciki.a kuma dauki slice daya a yanka bakinsa kadan a saka ajikin bakin kofin. Za’a sha da strew.