Majalisar Dattijan Najeriya ta yi watsi da buƙatar Shugaba Muhammad Buhari ta neman amincewa da wasu maƙudan kuɗaɗe da gwamnati ta karɓa da sunan rance daga Babban Bankin ƙasar.
Maƙudan kuɗaɗen dai sun zarce naira tirliyan ashirin da biyu.
Gwamnati ta yi ta karɓar kuɗaɗen ne a matsayin rance mai gajeren zango ko buƙatar kuɗi ta gaggawa tun kafin ta samu amincewar majalisar tarayya.
An dai ta da jijiyoyin wuya yayin zaman majalisar na ranar Laraba, saboda zargin da wasu ke yi cewa akwai rashin gaskiya a cikin lamarin.
Kuɗaɗen na wani asusu ne da ake kira Ways and Means a Ingilishi wanda ke bai wa gwamnati damar karɓar rance daga Babban Banki idan tana buƙatar kuɗi cikin gaggawa ko kuma buƙatar gajeren lokaci don gudanar da harkokinta na wasu kuɗaɗe da take sa ran samu amma aka samu jinkiri.
Rahotanni sun ce dokar da ta kafa asusun ta gindaya sharaɗin cewa duk kuɗin da za a bai wa gwamnati ta cike giɓin kuɗin da ta samu, ba za su wuce kashi biyar na kuɗin shigar da ta samu a shekarar da ta wuce ba.
Sai dai, tun bayan fara samun gagarumin ƙarancin kuɗaɗen shiga, sai gwamnati ta koma wajen babban banki tana samo kuɗi daga asusun Ways and Means tana gudanar da harkokin kuɗinta.
Sanata Ahmed Babba Kaita, ɗan majalisar dattijai daga mazaɓar Daura a jihar Katsina ya bayyanawa manema labarai cewa akwai sarƙaƙiya game da kuɗaɗen saboda an yi ta kashe su ba bisa ƙa’ida ba, ba kuma tare da sahalewar majalisa ba.
A cewarsa, “an yi amfani da ƙarfin gwamnati wajen yin yadda ake so, sai dai yanzu lamarin na neman ba da ruwa, an dawo an kawo mana cewa mu sa hannu kawai a wuce, wannan abu shi ne ya ƙi yiwuwa”.
Sai dai Sanatan ya ce ba wai yana nufin duka kuɗaɗen da aka kashe ne ba a yi amfani da su ta hanya mai kyau ba, “akwai waɗanda yawanci sata ne.”
Ya ba da misali da yadda wasu gwamnoni a baya-bayan nan suka nemi a ba su kuɗi, aka rasa inda za a samu kuɗin, saboda bankunan kasuwanci na cikin gida sun daina ba su bashi saboda ba su da kuɗin biya, amma sai suka yi ɗan waken zagaye suka garzaya wajen babban bankin ƙasa, suka shirya aka ba kowacce jiha naira biliyan 18.
“Suna cikin irin kuɗaɗen da aka ƙunso yanzu aka kawo zauren majalisa aka ce mu sa musu hannu, (amma) muka ƙi.”
Sanata Babba Kaita ya bayyana cewa a lokacin da APC ta hau kan mulki, irin waɗannan kuɗaɗe da ta gada daga gwamnatin PDP, bai fi naira tirliyan biyu zuwa huɗu ba, amma “yanzu ana maganar tirliyan 22,”
“Kuma abin da zai ƙara ta da maka hankali shi ne wannan kuɗin lokacin da aka fi karɓar su, (shi ne) cikin shekara biyun nan da ta wuce, nan ne aka fi yin almubazzaranci da wannan kuɗin.”
Majalisar dai ta buƙaci a zo a yi mata bayani dalla-dalla kan yadda aka kashe kuɗaɗen kuma kan haka ne ma ta kafa wani kwamiti na musamman da zai tuntuɓi ministar kudi Zainab Ahmed Shamsuna da gwamnan babban bankin Najeriya da sauran shugabannin hukumomin gwamnati da ke da ruwa da tsaki.
Ana sa rai kwamitin, a ƙarƙashin Shugaban masu rinjaye na majalisar dattijai Sanata Ibrahim Gobir, zai gabatar da rahotonsa ranar 17 ga watan Janairun sabuwar shekara.