Daga Jamila Sulaiman Aliyu
Taron da ake gudanarwa duk larabar karshen wata na hukumar Hisba ta jihar Kano a wannan karo ma ya gudana a harabar hukumar inda wannan karo ya zama na karshe a shekarar 2022 .
Babban kwamandan hukumar hisbah sheik Haroon muhd sani ibn sina ya ja hankalin dakarun hukumar ta bakin mukaddashinsa malam shehu Tasi’u Ishaq wanda ya wakilci kwamanda biyo bayan ziyarar aiki da kwamandan yake yi ayanzu haka a kasa Mai tsarki.
Malam shehu Tasi’u Ishaq ya ja hankalin dakarun hukumar dasu kasance cikin tsafta a ko da yaushe tare da bin dokoki da ka’idojin da aka gina hukumar ta hisbah a kansu.
Makaddashin kwamandan da makarrabansa, malama kulsum kasim mataimakiyar kwamandan hukumar a bangaren mata da malam Husaini Ahmad chediyar kuda mataimakin kwamandan hukumar a bangaren aiyukan musamman da kuma malam mukthar Usman maidu dukkansu sunba da hadin Kai wajen samun nasarar taron karshen watan.
Tunda farko sashen ladaftar da dakarun hukumar karkashin jagoranci malam Ibrahim sulaiman fagge sun tsaya Kai da fata akan ganin ko wanne Dan hisbah yazo taron cikin kayan aiki