Muhammadu Buhari zai halarci taron da Shugaban kasar Ghana ya kira na kasashen yankin Guinea
Jawabin da fadar Shugaban kasa ta fitar ya ta bakin mataimakin shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai ya ce jirgin Shugaban zai tashi ne a yau A matsayinsa na tsohon Shugaban kungiyar ECOWAS, Mai girma Buhari yana cikin masu jawabi
Adesina yace taron na musamman ne na kasashen yankin Guinea, wannan ne kuma karo na uku da za ayi irin wannan zaman.
“Shugaba Muhammadu Buhari zai bar Abuj zuwa Accra a ranar Talata, 25 ga watan Afrilu, domin halartar babban taron shugabannin kasashe da gwamnatocin hukumar kula da kasashen yankin tekun Guinea (GGC) wanda Shugaban kasar Ghana, Nana Akuffo-Ado ya kira.
Buhari zai sami rakiyar Daraktan Hukumar tattara bayanan sirri na kasa, Ambasada Ahmed Rufai Abubakar yana cikin ‘yan tawagar tare da wasu manyan jami’an gwamnati.
Zaman zai kunshi tattaunawa kan yadda za a wanzar da zaman lafiya tare da kawo karshen masu aikata mugayen laifuffuka a yankin kasashen Guinea.