Yan bindiga sun kai wa tawagar ministan Abuja hari a ranar Alhamis a yayin da suke wani atisaye a kan hanyar zuwa filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja.
An kwace babura na haya (acaba) kimanin guda 100 a yayin atisayen kamar yadda Vanguard ta rahoto
yayin da tawagar suka iso kusa da wurin wanke mota a Lugbe, wasu daga cikin yan acaban sun tattara kansu sun fara harbin yan tawagar da bindiga da kuma wasu muggan makamai.
Kayayyakin da tawagar suka kwato sun hada da bindiga kirar gida, pistol, adduna da wukake.
Babban mataimaki na musamman kan sa ido, tantancewa da aiwatarwa ga ministan Abuja, Attah Ikharo ya yi magana kan lamarin, ya ce: “Mun taho korar yan acaba ne a hanyar shiga filin jirgin saman.
Ministan na Abuja, Malam Muhammad Bello, ya bada umurnin a kore yan acaba domin an hana su bin manyan tituna amma sau da dama muna ganinsu suna satar hanya a babban titi, suna saba doka, hakan yana cutar da mutane don haka muka zo mu kore su a hanyar zuwa filin jirgin saman.” Ikharo ya yi tir da harin Da ya ke tir da harin da aka kai wa jami’an tsaron ya ce: “A wurin mu wannan ba sabon abu bane, mun saba ana kai mana hari. An sha kai mana hari.
“Kafin a kafa tawagar hadin gwiwa, yan acaba sun sha kawo mana hari, abu ne wanda ya saba faruwa a nan.”