Gwamna Yahya Bello zai ‘kwace Kamfanin siminti na Obajana daga hanun Dangote

Gwamnatin jihar Kogi karkashin jagorancin gwamna Yahya Bello, tace ta soma shirin karbe kamfanin simintin da ke Obajana daga hannun kamfanin Dangote Industries Limited.

A ranar Larabar nan aka rufe kamfanin simintin saboda sabani a kan hakkin mallaka. The Cable ta fitar da wannan rahoto a yammacin jiya.

Wani rahoto da aka gabatarwa Gwamnan jihar Kogi, ya nuna Gwamnati ba ta yarda kamfanin simintin Dangote ya mallaki kamfanin Obajana ba.

A rahoton da Sakatariyar gwamnatin jihar, Folashade Ayoade ta gabatar, ta nuna cinikin Dangote da kamfanin simintin Obajana bai tabbata ba.

SSG tace satifiket din da kamfanin ya yi amfani da su a lokacin yana karkashin Jihar Kogi ne Aliko Dangote ya yi aiki da su wajen cin bashin N63bn.

Ayoade tace kwamitinta da ya yi bincike a kan lamarin ya bada shawara ga gwamnatin Kogi ta karbe kamfanin daga hannun Alhaji Aliko Dangote.

Gwamnatin Kogi tayi bincike a kan saida kamfanin simintin Obajana da aka yi a shekarun baya Binciken da SSG ta gudanar ya nuna ba Dangote Industries Limited suke da mallakar kamfanin ba Ana zargin an saba lamba wajen sayen kamfanin simintin, kuma majalisar Kogi ba ta san da cinikin ba

Rahotanni sunce sakatariyar gwamnatin ta jagoranci kwamitin da ya fadawa gwamnati ta karbe har da ribar kudin da Dangote ya rika samu daga Obajana.

Shawarar kwamitin Folashade Ayoade “Babu shaidar da ke nuna Dangote Industries Limited ya biya jihar Kogi kudi wajen mallakar kamfanin Obajana Cement Company Plc.

Babu kudin da aka biya jihar a matsayin ribar da aka samu daga lokacin kamfanin Dangote Cement Company ya fara aiki zuwa yanzu.

Satifiket din mallaka uku na kamfanin Obajana Cement Company Plc sun tabbatar da gwamnatin Kogi ce kadai take da hakkin mallaka.”

Daily Nigerian ta ruwaito shugaban majalisar dokokin Kogi, Matthew Kolawole yana cewa an saida kamfanin ne ba tare da sanin ‘yan majalisar jihar ba.

Kolawole yace ba za a iya saida dukiyar gwamnati ba tare da sa bakin majalisar dokoki ba, kuma an saba doka wajen saida hannun jarin Obajana.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments