Sojojin Najeriya sun dakile harin ba-zata da ’yan bindiga suka kai musu a sansaninsu dake Kankomi na karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna
Dakarun sun ragargaji ‘yan bindigan inda suka bibiyesu har zuwa sansanoninsu tare da halaka 2 daga ciki sannan suka samo makamai da babura
Sai dai cike da abun takaici, ‘yan bindigan sun halaka wasu mutum 3 a kan hanyarsu ta tserewa daga rugugin luguden wutan sojojin